Shirin Rana na 08/07/2024🎤
😊 Fauziyyah Dauda ce zata gabatar da shirinmu na rana da misalin karfe biyu agogon Najeriya da Nijar, karfe 1 agogon GMT da Ghana.
👍Ga jerin rahotanni da za mu kawo muku inda za ku iya sauraro kai tsaye a babban shafinmu na intanet a nan👉 🔗www.dw.com/......
👉 Hukumomin tsaro na kasar Jamus sun sanar da aniyarsu ta rufe sansanin sojin sama na kasar da ke a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.
👉Samoa: DW Hausa ta yi hira ta musamman da ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya Abubakar Atiku Bagudu kan yarjejeniyar Samoa da wasu ke yi wa kallon ta neman kare masu auren jinsi guda ne.
👉Manyan kasashen duniya irinsu Amurka da Rasha da Jamus da sauransu na kara narka kudi kan fannoni daban-daban a nahiyar Afirka. Shin me suke nema? Muna tafe da rahoto.
👉Tanzaniya ta tashi makiyaya 'yan kabilar Masai daga yankunansu na gado tun kaka da kakanni a wani yunkuri da gwamnati ta ce na bunkasa harkokin gandun daji ne.
👂✍Za ku iya sauraron shirin da kuma bayyana ra'ayoyinku a nan shafinmu na Facebook.
Sai mun ji daga gareku 👂
5 окт 2024